Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Sanawar da gwamnatin Sojin Mali ta fitar ta bayyana Keita a jerin gwarzayen shugabanni da Mali ta gani a tarihi yayinda ta aike da ta’aziyyar shugaban wanda ta ce ya rasu sakamakon doguwar jinya da ya yi.
Gwamnatin mulkin sojan kasar ta kuma ba shi dukkan wasu hakkoki a matsayinsa na tsohon shugaban kasar Mali.
Tuni dai shugabannin kasashe suka fara aike da sakon gaisuwa ga rashin na Boubacar Keita da ake yiwa lakabi IBK, ciki har da Macky Sall na Senegal da tsohon shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou wadanda suka bayyana Keita a matsayin jajirtacce.
IBK ya mulki Mali daga 2013 gabanin hambarar da kujerarsa a watan Agustan 2020 da sojoji sukayi.
Kwamitin ceton jama'ar kasar (CNSP) ya hambarar da Keita a ranar 18 ga watan Agustan shekarar 2020, bayan watanni jama’a na zanga-zanga a kan titunan kasar, inda suke kalubalantar gwamnatinsa.
Ya rasu yana da shekaru 76.
Har yanzu dai ba a san musabbabin mutuwar tasa ba.
342/